Instagram story viewer> @bashtvmedia> Posts
3K
followers
30
following
please like and follow 🙏
Labran duniya da halshen hausa
POSTS STORIES REELS TAGGED
Download All
🚨 Gwamnan Kaduna Ya Yi Afuwa Ga Fursunoni 27

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi afuwa ga fursunoni 27 da ke zaman jiran hukunci a gidajen gyaran hali daban-daban a jihar, domin bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai.

Gwamnatin jihar ta ce adadin fursunonin da suka amfana da ikon afuwar gwamnan tun bayan hawansa mulki a 2023 ya haura 500. Haka kuma, an kashe sama da Naira miliyan 300 wajen biyan tara da diyya domin taimaka wa wasu fursunoni da suka cancanta su samu ’yanci.

#hausa #BreakingNews #fypシ゚viralシ by @bashtvmedia
0
2 days ago
Download
🚨NAFDAC ta hana amfani da maganin KETOCONAZOL saboda yana lalata Hanta!.

#hausa #labaranduniya #nafdac #news by @bashtvmedia
3
5 days ago
Download
🚨GARGADI!!,GARGADI!!.

NAFDAC Ta Dakatar da rijistar  maganin Ketoconazole Na Sha Saboda Hadarin Lalata Hanta

Hukumar kula da ingancin magunguna da abinci ta Najeriya (NAFDAC) ta dakatar da rijistar maganin Ketoconazole na sha sakamakon hadarin da yake da shi na haddasa mummunar illa ga hanta, wanda ka iya kaiwa ga mutuwa.

Matakin ya shafi maganin Ketoconazole na sha, ciki har da allunan 200mg. Sai dai, dakatarwar ba ta shafi man shafawa, kirim da shamfu masu dauke da wannan sinadari ba, wadanda har yanzu suna da izinin amfani.

Wannan mataki ya yi daidai da matakan da hukumomin kula da magunguna na Amurka (FDA) da Turai (EMA) suka dauka a baya, saboda hadarin da maganin ke da shi na lalata hanta.

NAFDAC ta bukaci likitoci da sauran ma’aikatan lafiya su shawarci marasa lafiyar da ke amfani da maganin da su koma wurin likitocinsu domin samun wasu magunguna masu aminci.

Hukumar ta kuma gargadi jama’a da kada su sauya magungunansu ba tare da shawarar likita ba.

Duk da haka, ana iya amfani da Ketoconazole na sha wajen magance wasu cututtuka na musamman, kamar Cushing’s syndrome, amma sai karkashin kulawar kwararrun likitoci.

Matakin na NAFDAC na da nufin kare lafiyar jama’a daga mummunar illa ga hanta, musamman ga masu amfani da maganin wajen magance cututtukan fungus na yau da kullum. by @bashtvmedia
1
9 days ago
Download
🚨Mafita guda ga lafiyar mu.

#hausa #trend by @bashtvmedia
5
14 days ago
Download
🚨Izala ba jamiyar siyasa bace, inji Sheikh Bala Lau. 

 #Hausa  #JIBWIS  #trending  #fypシ゚viralシ by @bashtvmedia
2
15 days ago
Download
🚨Tarihin Mutunin da ya samar da kamfanin Indomie.

 #Hausa  #documentary  #trending  #fypシ゚viralシ #foryouシ  history @indomie_nigeria by @bashtvmedia
6
15 days ago
Download
🚨 Zamfara Ta Kulla Yarjejeniya Don Fara ziraga-zirgar Jiragen sama daga Gusau zuwa Abuja.

Gwamnatin Jihar Zamfara ta sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da kamfanin XEJet Limited domin fara zirga-zirgar jiragen sama kai tsaye tsakanin Filin Jirgin Sama na Gusau da Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Ana sa ran kamfanin XEJet zai fara zirga-zirgar jiragen a watan gobe, sau biyu a mako.

Gwamnatin ta ce sabuwar hanyar za ta inganta zirga-zirgar mutane da kayayyaki, tare da taimakawa wajen bunkasa kasuwanci, zuba jari da yawon bude ido a jihar.

Mataimakin Gwamnan Zamfara, Mani Mummuni, ya ce fara zirga-zirgar jiragen zai kara saukaka shiga Zamfara tare da taimakawa wajen jawo masu zuba jari.

#hausa. #brakingnews #Zamfara by @bashtvmedia
1
15 days ago
Download
🚨Rayuwar matasa a Najeriya na cikin hatsari saboda WAZA (VAPE).

#hausa #bashtvmedia #fypシ❤️💞❤️ #trend by @bashtvmedia
4
19 days ago
Download
🚨Tarihin Sheikh professor Abdullahi Sale Usman Pakistan.

 #hausa  #history  #documentaryfilm #fypシ゚viralシ #trendingnow by @bashtvmedia
0
22 days ago
Download
🚨Rayuwar mu na cikin babban hatsari.

 #Hausa  #trending  #fypシ゚viralシ #healthyhabits by @bashtvmedia
6
23 days ago
Download
🚨Gaskiyar girman nahiyar Afirka ta bayyana. by @bashtvmedia
0
a month ago
Download
🚨Kaduna State drone shot.

#fypシ゚viral #dronevideo #kaduna #fypシ by @bashtvmedia
0
a month ago
Download
×

Download all media on this page

Photos Videos
back to up